Bincike a kan jirgin Malaysia

Hakkin mallakar hoto b
Image caption Tarkaccen jirgin MH370

Jami'ai a kasar Faransa na ci gaba da bincike domin bindiddigin yadda aka yi jirgin kasar Malaysia dauke da mutane 239 ya yi batan-dabo.

Yanzu haka suna gudanar da binciken ne a kan wani tarkacen jirgin da aka samu ranar Laraba a tsibirin kasar ta Faransa da ke tsakiyar teku.

Kwararru a fanni jiragen sama a Amurka sun ce suna da yakinin cewa tarkacen yana da alaka da jirgin Malaysian da ya bata.

Batan da jirgin na kasar Malaysia ya yi ya kasance wani abu mai kama da dabo ga fannin tashi da saukar jirage a duniya wanda kuma daruruwan iyalai suke jiran sanin gaskiyar al'amarin.

Kawo yanzu dai an kwashe watanni 16 a na ta faman neman sa amma kamar an aika bawa garinsu.

A watan Maris din shekarar 2014 ne dai jirgin wanda ya tashi daga Kuala Lumpur ya nufi Beijing ya yi batan dabon.