'A kwashe 'yan gudun hijira daga makarantu'

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army

Majalisar wakilan Najeriya ta amince da wani kuduri na yin kira ga gwamnatin kasar da ta sauyawa dubban 'yan gudun hijirar da ke fakewa a makarantun birnin Maiduguri matsuguni, domin bai wa dalibai damar ci gaba da karatu.

Majalisar ta ce ana tauyewa dubun dubatar yara 'yan makaranta damarsu ta samun ilmi a birnin, saboda yadda makarantun nasu ke ci gaba da kasancewa matsugunai ga wadanda rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu.

Hon. Garba Chede Hammanjulde ya shaidawa BBC cewa 'muna son a yi musu sansani wanda za su tsuguna, kafin a samar musu wajen da za su zauna na dindindin'.

Rikicin Boko Haram dai ya raba mutane fiye da miliyan daya da gidajensu.