Kasashen Sahel 4 na taro kan tsaro

Hakkin mallakar hoto
Image caption Mahammadou Issoufou shugaban Nijar

Wasu kasashe hudu na yankin Sahel da suka hada da Nijar da Mali da Burkina Faso da Muritaniya suna wani taro na kwanaki biyu a Yamai domin tattaunawa a kan matakan da suka dace su dauka domin kyautata tsaro a kan iyakokinsu.

Hukumar kula da bakin haure ta duniya OIM ce ta shirya taron tare da hadin gwiwar kasar Japan karkashin wani tsarin da OIM ta fitar.

Wakilin gwamnatin Mali a wajen taro Musa Ibrahim Turai, ya ce kalubalan tsaro da kasashen hudu ke fama da su kamar fataucin miyagun kwayoyi da fashi da makami da tururuwar 'yan ci rani masu son tsallakawa Turai, sune suka tilasta wa kasashen bijiro da taron domin daukar matakan gaggawa.

Tun a baya ne hukumar OIM ta fitar da tsarin kula da kan iyakoki tare da hadin kan kasashen hudu, sakamakon matsalolin da yankin Sahel ke fuskanta.

Hadiza Barau tsohuwar jami'a ce ta OIM reshen Nijar, ta shaida wa BBC cewa shirin ya tanadi gina cibiyoyin bincike a kan iyakokin kasashen hudu.