Rayukan da aka salwanta wurin safarar mutane

Miliyoyin maza da mata da yara a duniya, na fuskantar matsalar safarar mutane da ake yi da su, ta hanyar cinikayya ko kuma karuwanci da bautarwa.

Wannan safarar mutane da ake yi ta zagaya duniya kuma harkar ta bunkasa.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Kungiyar kwadago ta duniya ta kiyasta cewa bautarwa na samar da dala biliyan 150 watau Euro biliyan 96 a kowace shekara, yayinda kaso biyu cikin uku na kudaden na zuwa daga karuwanci watau dala biliyan 99.

Amma shin su waye ke zakulo wannan lissafi?

Kemi da Bilkisu 'yan Najeriya ne, Jane kuma daga Biritaniya ta ke, ita kuma Gabby ta fito daga Amurka, dukkaninsu sun shiga hannun masu safarar mutane.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Ga labarin Kemi- Nigeria

Ana sayar da dubban manya da 'yan mata daga Afrika ta yamma duk shekara, kuma yawanci Turai ake kai su.

Ofishin laifukan miyagun kwayoyi ta Majalisar Dinkin Duniya ya gano wadanda aka yi safarar su galibi daga Najeriya ne, daukacin kaso 10 cikin 100 ana tilasta masu aikin karuwanci ne a yammacin Turai.

A kudancin Najeriya, birnin Benin ne kan gaba a wannan harkar, inda har suke da cibiyoyin sadarwa da gine-ginen da aka yi domin safarar mutane.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An san birnin Benin da ke kudancin Najeriya ita ce cibiyar safarar mutane a kasar.

A nan, masu safarar suna nemo matan da suke burin keta hazo, su kwadaita su da alkawuran samun aiki da karin ilimi.

Za a sama masu takardun jabu kuma a gaya masu za su biya kudin tafiyarsu bayan sun isa kasar.

Bayan an shigar dasu, sai a tilasta masu wasu yin tsafe-tsafe, domin a tabbatar da amincewar su.

Wata mata mai safarar mutane a Benin, ta bayyana yadda suke safarar 'yan mata, inda suke tube su tsirara, su yi masu aski sannan a kai su wurin boka a wani biki na rantsar da su.

Ta ce "Tsoro na shiga zukatan 'yan matan a dalilin wadannan abubuwa da aka masu."

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Labarin Bilkisu da Jane- Biritaniya

Daruruwan mutane da ake safara daga Najeriya suna zuwa Biritaniya ne, inda suke fuskantar rayuwar karuwanci da bauta a gidajen mutane.

Hukumar laifukan kasa ta Biritaniya ta ce mutane 244 cikin 2,340 da suka kai kara wurin hukuma a kan an yi safarar su--daga Najeriya suke, kuma an samu karin kaso 31 cikin 100 a kan shekarar da ta gabata.

Kasar da ta fi kowacce yawan mutanen da aka yi safarar su, ita ce Albania.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Bilkisu tana cikin wadanda aka yi safararsu da rufa ido daga Najeriya.

Tun tana shekara 15 aka bautar da ita, tayi shekara goma tana aiki sa'o'i da dama ba a biyan ta ko anini.

Kawun ta yayi mata alkawarin za ta ci gaba da karatu, kuma za ta samar wa iyayenta kudi da kuma sauyi mai inganci a rayuwarta.

'Zagaye a Turai'

Halin da Bilkisu ta shiga, ya bambamta da halin da yawancin wadanda aka yi safarar suka shiga a Biritaniya, inda ake cinikinsu a cikin kasar.

Gwamnatin Biritaniya tana zargin akwai a kalla yara 13,000 da ake cin zarafin su ta wannan hanyar a Biritaniya.

Image caption Akalla yara mata 13,000 ake cin zarafin su ta hanyar karuwanci a Biritaniya.

An ci zarafin Jane tun tana shekaru 13, bayan haka kuma ta shiga karuwanci a Biritaniya ta wannan hanyar.

Tun tana makaranta abin nata ya fara, inda wani tsoho dan shekara 70 ya fara mata kyauta kala-kala.

Bayan haka sai ya bukace ta da ta bayar da kanta domin ta biya shi kyautar tasa.