Chadi za ta mai do da hukuncin kisa

Hakkin mallakar hoto
Image caption Chadi na fuskantar hare-hare a baya-bayan nan daga kungiyar Boko Haram

Majalisar dokoki a Chadi ta kada kuri'ar mai do da hukuncin kisa a kan 'yan ta'adda, bayan da aka soke hukuncin watanni shida da suka gabata.

Matakin ya biyo bayan hare-haren da mayakan Boko Haram suke kai wa a 'yan kwanakin nan daga makwabciyar kasar Najeriya.

'Yan adawa da kuma kungiyoyin fararen hula sun soki dokar yaki da ta'addancin, suna masu cewa za a yi amfani da ita ne wajen tauye 'yancin fararen hula.

Chadi dai ta jibge dubban dakarunta tare da sojoji daga kasashen Najeriya da Kamaru da kuma Nijar domin yaki da Boko Haram.