'Yan kunar bakin wake sun mutu a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Nigeria na ci gaba da fuskantar hare haren mayakan Boko Haram

Hukumar bayar da agajin gaggawa a Najeriya ta ce 'yan kunar bakin wake shida ne suka mutu bayan bama baman da suke dauke da su sun tashi a Maiduguri da ke Najeriya.

Babban jami'in hukumar da ke kula da arewa maso gabashin Najeriya, Alhaji Muhammadu Kanal, ya shaida wa BBC cewa akalla mutane 11 ne suka samu raunuka kuma an kai su asibiti.

A cewar sa, lamarin ya faru ne a Gambarou Kasuwa, 'kwastam area', a Maiduguri lokacin da bama baman da 'yan kunar bakin wake ne da ke cikin babur mai kafa uku suka tashi.

Ya kara da cewa bama baman sun tashi ne kafin mutane su tayar da su a kasuwar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar dukkan su.

Wani da ya ganewa idanunsa ya ce ya ga gawawwakin mutanen da suka mutu sun yi kacha-kacha.

Birnin na Maiduguri dai ya sha fama da hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram.