Museveni yana neman tazarce a Uganda

Image caption Museveni ya shafe shekaru 30 yana mulki a Uganda

Shugaban Uganda, Yoweri Museveni wanda ke kan mulki tun shekarar 1986, ya bayyana aniyar sa ta sake tsayawa takarar shugabancin kasar a shekara mai zuwa.

Tsohon Firai Ministan kasar, Amama Mbabazi wanda a baya ake saran zai zama dan takarar jam'iyya mai mulki, a ranar Juma'a ya janye aniyarsa ta tsayawa takara.

Sai dai ya ki sukar Mr Museveni a matsayin wanda ya ki sauka daga kujerar mulki.

Hakan na zuwa kwanaki kadan bayan da Shugaban Amurka, Barack Obama ya yi jawabi ga kungiyar Tarayyar Afrika inda ya bukaci shugaban da suka dade a kan mulki su ba da wuri domin wasu su hau.