An hallaka jariri Bafalasdine

Image caption Ana zargin cewa da gan-gar aka saka wuta a gidansu jaririn

An gudanar da jana'izar wani yaro Bafalasdine mai shekara daya da rabi, wanda aka kashe bayan da aka cinna ma gidansu wuta a gabar yammacin kogin Jordan.

Ana kyautata zaton cewa wasu Yahudawa 'yan kama-wuri zauna ne suka kai harin, inda aka raunata iyayensa.

Firayi Ministan Isra'ila, Benyamen Netanyahu ya ce abin da aka aikatan ta'addanci ne.

Falasdinawa na zargin gwamnatin Isra'ila da kawar da kai, da kuma kin hukunta Yahudawa 'yan kama wuri zauna.

An dade ana zaman dar-dar tsakanin Falasdinawa da Yahudawan Isra'ila.