An samu kwarin gwiwa a yaki da Ebola

Hakkin mallakar hoto
Image caption An yi gwajin maganin a kan dubban mutane ba tare da ba ta lokaci ba.

Hukumar lafiya ta duniya ta yabawa sakamakon gwaje-gwajen allurar rigafi kan cutar Ebola da aka yi a kasar Guinea wanda ya samar da kariya 100 bisa 100 ga mutane.

Hukumar ta ce duniya na gab da samun allurar rigafin da za ta yi tasiri a kan cutar ta Ebola.

An yi gwajin maganin a kan dubban mutane ba tare da ba ta lokaci ba, bayan da wani na kusa da su ya kamu da cutar ta Ebola kuma bayan kwanaki goma da yin alurar babu wani a cikinsu da ya kamu da cutar.

Har yanzu ba'a bayar da izinin amfanin da allurar rigakafin ba, sai dai an soma shirye-shiryen rarraba maganin a kasashen duniya.

Mutane sama da 11,000 ne suka rasu bayan kamuwa da cutar Ebola tun barkewar cutar a kasar Guinea a shekarar 2013.