Majalisar koli ta Taliban ta soki zaben Shugaba

Image caption Rikicin shugabanci a kungiyar mayakan Taliban

Wani mai magana da yawun majalisar koli ta 'yan Talliban dake Afganistan ya fadawa BBC cewa ba a tuntube su ba, a zaben jagoran kungiyar da aka gudanar a kwanan nan, bayan mutuwar shugaban kungiyar Mullah OMar

Mai magana da yawun majalisar Mullah Abdul- Manan Niazi, ya ce majalisar zata gudanar wani Taro a yanzu, domin zabar sabon Shugaba

A ranar Alhamis ne majiyoyin kungiyar Taliban suka ce an zabi Mullah Mansur a matsayin sabon jagoran kungiyar

Wasu fitattun kungiyar Taliban sun soki wasu masu goyan- bayan Pakistan da tilasta shugabancin Mullah Mansur akansu