Ana tababar rasuwar Jalaluddeen Haqqani

Tutar masu Jihadi
Image caption Babu tabbaci dai akan mutuwar ta Jalaluddeen Haqqani.

Ana cigaba da rudani kan rahotannin mutuwar Jalaluddin Haqqani, shugaban kungiyar masu kaifin ra'ayin addinin Islama, ta Haqqani.

Wata sabuwar sanarwa a daya daga cikin shafukan yanar gizon kungiyar Taliban ta ce babu kamshin gaskiya game da mutuwar tasa, hasali ma yana nan cikin koshin lafiya, bayan da a baya ya yi fama da wata rashin lafiya.

Amma kuma a ranar Jumma'a, wasu majiyoyi da dama na kungiyar Taliban din sun ce Jalaluddin Haqqani ya yi akalla shekara guda da mutuwa.