'Za a murkushe Boko Haram zuwa karshen 2015'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Buhari ya lashi takobin ganin bayan Boko Haram

Mai bai wa Shugaban Nigeria shawara kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya fadawa BBC cewa a karon farko Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya na fatan za a murkushe Boko Haram zuwa karshen shekara.

Shugaba Muhammadu Buhari ya furta hakan ne a ziyarar da ya kai zuwa Jamhuriyar Benin a ranar Asabar.

Ziyarar wani bangare ne na ci gaba da tuntubar shugabannin kasashe makwabtan Najeriya dangane da yadda za a shawo kan matsalolin tsaron da suke fama da su.

Malam Garba Shehu ya kuma fadawa BBC cewa Jamhuriyar Benin ta kuma sha alwashin taimakawa kasashen raya tafkin Chadi a yakin da suke yi da mayakan Boko Haram.

Jamhuriyar Benin ta ce zata ba da gudummuwar sojoji 800 domin wannan yaki.