Ba-Amurke ya harbo jirgi mara matuki a gidansa

Hakkin mallakar hoto AP

Wani mutum a Amurka ya harbo wani jirgi mara matuki dake shawagi a saman lambun gidansa

Daga bisani 'yan sanda sun tsare William Meredith, daga Hillview, Kentucky

Kafofin yada labarun yankin sun ce an tsare shi sannan za a tuhume shi

Mr Meredith ya fadawa BBC cewa ya budewa jirgin wuta sau uku kafin ya fado cikin itatuwan dake bayan gidansa.

A ranar Alhamis ne diyar Mr Meredith ta shigo gida daga lambunsu na bayan gida, inda ta fadawa mahaifinta cewa taga wani jirgi marar matuki

Mr Meredith ya bayyana cewa jirgin mara matuki na shawagi ne a saman unguwarsu.

Da jirgin kuma ya kawo ga saman gidansa, sai ya harbo shi

Harbi uku daga wata karamar bindigarsa ne ya kakkabo jirgin daga sama

Ya ce 'sai na nemi tsira, na maida bindiga ta, na ji cewa abinda na yi ya dace da 'yanci na a matsayina na dan-kasa domin kare kadara ta'

Ya kara da cewa ya damu cewar jirgin marar matuki na yin kuste ne ga sirrinsa da na 'ya'yansa mata, kuma wannan shi ne karon farko da ya ga jirgi mara matuki ya na shawagi a yankin

Daga baya ne wasu mutane hudu tare da mai jirgin, suka durfafi Mr. Meredith a wajen gidansa

Mr. Meredith ya ce sun fusata game da abinda na yi, harma mu ka yi musayar kalamai'