Wanda ya kirkiro Facebook zai samu karuwa

Hakkin mallakar hoto Facebook

Babban jami'in kamfanin Facebook Mark Zuckerberg da kuma matarsa, Priscilla Chan na tsammanin samun karuwar 'ya-mace.

Ma'auratan sun sanar da hakan ne a shafin Mr Zuckerberg na facebook

Ya rubuta cewa ' Priscilla da ni na da wani labari mai dadi, shi ne muna tsammanin samin karuwar 'ya-mace

Zuckerberg ya rubutawa masu bin sa a shafin mutane miliyan 33.

Ya kuma bayyana cewa cikin mai dakinnasa ya zube har sau uku a baya, amma ya ce a wannan karon yana ganin hatsarin faruwar hakan kadan ne.

Sai dai bai bayyana lokacin da suke sa ran haihuwar ba