An sake gano wani bangaren Jirgin MH370

Wani bangare na MH370 da aka fara ganowa. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jami'ai a Australia na da kwarin gwiwar tarkacen jirgin da aka gano a Reunion na jirgin saman Maleysian ne.

'Yan sanda a tsuburin tekun India na Reunion, sun sake gano wani bangare da ake kyautata zaton na tarkacen jirgin Malaysia MH370 ne da ya yi batan dabo fiye da shekara guda.

Jami'an sun ce abinda suka dauko daga cikin tekun na kama da kofa, wadda aka yi rubutu da haruffan turanci a jikinta.

An dai gano wannan tarkace ne a kudancin birnin St Denis, ba kuma tare da bata lokaci ba an mika shi ga hukumomi dan a fara gudanar da bincike.

A ranar larabar da ta gabata ne aka samu wani bangare na jirgi samfurin Boeing 777, wanda ake kyautata zaton wani banagre ne na jirgin Malaysia MH370 da ya bata a watan Maris din shekarar da ta wuce, a lokacin da ya taso daga Kuala Lampur zuwa Beijing.