Sojin Najeriya na nazarin shari'ar da ake yi wa jami'ansu

Sojojin Nigeria. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rundunar Sojin ta dauki wannan mataki ne sakamakon korafin da ake yi kan hukuncin da aka yankewa wasu daga cikin sojojin.

Rundunar Sojin Najeriya ta ce za ta sake nazarin wasu shara'o'in da ke gaban kotunanta don tabbatar da cewa an yi adalci ga sojojin da ake musu shari'a.

Kakakin rundunar sijin kasa ta Najriya, Kanar Sani Usman Kukasheka ya tabbatar wa BBC cewa cikin shara'o'in da za a sake dubawa har da wadanda suka shafi wasu daga cikin sojojin da ake tuhuma da nuna rashin da'a a yakin da kasar ke yi da masu ta-da-kayar-baya.

A cewar Kakakin, an dauki wannan matakin ne sakamakon korafe-korafen da rundunar ta samu daga mutane da dama a Najeriya, kuma wasu daga cikin korafe-korafen ma ba su shafi yakin da ake yi da 'yan boko-haram ba.

Kotunan sojin Najeriya dai sun yanke wasu hukunce-hukunce, inda aka sallami wasu sojojin daga aiki yayin da wasu kuma ake ci gaba da yi musu shari'a.

Wasu daga ciki dai an kama su ne da laifin gudu daga fagen daga, kodayake su ma sun yi zargin cewa ba su da isassun kayan fadan da za su tunkari mayakan boko-haram.

A 'yan kwanakin ne tsohon hafsan hafsoshin Najeriya, Air Marshal Alex Badeh mai ritaya ya bayyana cewa sojin Najeriyar sun yi fama da rashin kayan yaki.

Sai dai Kakakin rundunar sojin kasa ta Najeriyar ya ce ba zai iya cewa matakin da aka dauka na sake duba shara'o'in ko suna da nasaba da wannan furucin da tsohon hafsan sojojin ya yi ba.