Abubakar Shekau ya yi layar zana

Hakkin mallakar hoto Boko Haram Video
Image caption Boko Haram ba ta ce komai ba a kan makomar Shekau

Kungiyar Boko Haram ta kara fitar da wani sabon bidiyo, ba tare da an nuna shugabanta Abubakar Shekau ba.

Hakan na kara saka ayar tambaya a kan makomar Shekau.

Rabon da a ji duriyar Shekau tun a watan Maris, inda ya fitar da sakon yin mubaya'a ga kungiyar IS mai ikirarin kafa daular Musulunci.

A bidiyon mai tsawon mintuna takwas, wani matashi ya bayyana cewar "Muna nan a duk wuraren da muke a baya."

Bidiyon kuma ya nuna 'yan Boko Haram sun kai wa jami'an tsaro hari, inda suka kwace makamai sannan suka yi wa wani mutumi mai kayan 'yan sanda yankan rago.

'Shekau ya yi layar zana'

A watan Yuni ma Boko Haram ta fitar da bidiyo amma babu Shekau a ciki.

Hakkin mallakar hoto BOKO HARAM
Image caption A bidiyon watan Yuni ma ba a ga Shekau ba

Masu sharhi na ganin cewar watakila Shekau ya boye ko kuma an ji masa rauni ko kuma an kashe shi.

Sai dai bidiyon alama ce da ke nuna cewar mayakan Boko Haram ba za su ba da kai bori ya hau ba.

Bidiyon -- wanda aka fitar a ranar Lahadi, ya nuna tsagwaron rashin imani inda wani matashi ya yi magana da Hausa, amma bisa alamu dan kabilar Kanuri ne kamar Shekau.