Masu gidajen haya za su kori 'yan ci-rani

Image caption 'Yan ci-ranin Biritaniya.

Gwamnatin Biritaniya ta sanar da wani shiri da zai dorawa masu gidajen haya a Ingila alhakin korar 'yan-cirani daga cikin gidajensu, idan har suka kasa samun amincewar hukumomi na mafakar da suka nema.

Ministan al'ummomi na Biritaniya Greg Clark, ya ce masu gidajen haya wadanda basa bincikar matsayin wadanda ke haya a gidajensu, ka iya fuskantar hukuncin daurin shekaru biyar cif a gidan yari

Ya ce wannan doka da aka gabatar, zata yi maganin masu- gidajen da ke samun kudade ta hanyar bakin da suke shiga kasar ba bisa doka ba.

Kalamansa, na zuwa ne bayan damuwar da ake ta nunawa game da yunkurin da 'yan ci-rani suke yi ko ta halin kaka, na shiga cikin Biritaniyan a tashar jiragen ruwa ta Calais da ke kasar Faransa .

Wannan dai ba shi ne karon farko da gwamnatin masu ra'ayin mazan jiya ke yunkurowa domin magance matsalar 'yan ci-rani da suke zaune cikin kasar ba bisa ka'ida ba.

Ko a shekarar 2013 ma, an yi irin wannan yunkuri.