An bukaci 'yan Burundi su kawar da kai

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Pierre Nkurunziza

Mahukunta a kasar Burundi sun yi kira ga 'yan kasar da su kwantar da hankulansu bayan wasu 'yan bindiga sanye da kakin soji sun harbe har lahira daya daga cikin Janar-janar na sojin kasar da ke da karfin fada-aji a ranar Lahadi.

Kakakin shugaba Pierre Nkurunziza, Mr Gerve Abehayo, ya ce duk wata ramuwar gayya da za a yi kan kisan da aka yi wa Janar Adolphe Nshimirimana, to lamarin zai wargaza zaman lafiyar da ake da shi a kasar.

"Wannan babban al'amari ne a gare mu, amma rundunar sojin kasar nan za ta ci gaba da kasancewa mai karfi, wacce kan ta ke hade," in ji Abehayo.

Don haka kisan da aka yi wa Janar daya, ko ma wasu da dama ba ya nufin an karya lagon kasarmu.

A watan jiya ne dai Mr Nkurunziza ya lashe zaben kasar mai cike da kace-nace, wanda gabaninsa aka kwashe kwana da kwanaki ana tarzoma.