An gudanar da gwaji kan cutar dajin tumburkuma

Hakkin mallakar hoto Douglas Fearon
Image caption Cutar daji mai kama tumburkuma

Masana kimiyya a Ingila da Sipaniya sun gudanar da wani gwaji wanda suka yi imani cewa zai taimaka wajen gano cutar dajin tumburkuma wato Pancreas, kafin ta yi tsanani.

Masana kimiyyar sun bayyana hakan da cewa wani ci gaba ne saboda a yanzu haka cutar tana saurin kisan mutane.

Gwajin yana duba yanayin sinadaran gina jiki a cikin fitsari sau uku kuma zai nuna yadda cutar ke yaduwa nan da nan fiye da yin hoton wajen wato scanning, ko kuma gwajin jini.

Zuwa yanzu dai an tabbatar da cewa gwajin ya yi tasiri kashi 90 bisa 100.

An kuma fara gudanar da wasu manyan gwaje-gwajen da suka hada da mutanen da kwayoyin halittarsu ke nuna cewa suna cikin hadari na kamuwa da cutar.