Ana adawa da rufe shafukan batsa a India

Image caption An rufe shafukan intanet masu nuna batsa a Indiya

Masu amfani da intanet a indiya suna nuna adawa kan rufe daruruwan shafukan yanar gizo na batsa da aka yi, bayan da gwamnatin kasar ta bayyana su da cewa suna bata tarbiya.

A makon da ya gabata ne gwamnati ta bai wa kamfanonin da ke samar da hanyoyin sadarwa umarnin rufe dukkan shafukan da ke nuna batsa, domin samar da kyakkyawar tarbiya a tsakanin al'umma.

Hakan ya biyo bayan wani mataki da kotun koli ta Indiya ta dauka ne domin hana amfani da shafukan batsa a intanet, saboda a cewarta, mutane suna da damar da za su kalli wadannan shafuka a asirce.

'Yan adawa sun ce dokar ta keta 'yancin dan adam kuma ba za a iya aiwatar da ita ba, saboda mutane za su iya duba shafukan a wasu hanyoyin intanet na kasashen waje.