Yadda za a magance sauyin yanayi - Obama

Hakkin mallakar hoto
Image caption Obama ya ce ya kamata a sauya tsarin da ake bi

Shugaban Amurka Barack Obama ya kaddamar da wasu manyan shirye-shirye a kan yadda za a mangace matsalar sauyin yanayi.

A cewarsa hakan ne babban kalubalen da ke fuskantar da al'umar gaba da kuma tsaron kasa.

"Wannan al'uma ta yanzu ita ce ya kamata ta kawar da matsalar ta sauyin yanayi, amma Amurka za ta iya, kuma ya zamar mata wajibi ta dauki matakin magance matsalar," in ji Obama.

A shirin nasa ya kunshi yadda Amurka za ta rage yawan hayakin da ake fiitarwa a masana'antu da kusan kashi daya bisa uku, ragin da ya fi wanda a da aka tsara za a yi.