Saraki ya kai ziyara Maiduguri

Hakkin mallakar hoto bukola
Image caption Sanata Saraki ya ce suna tare da 'yan jihar Borno

Shugaban majalisar dattawan Nigeria, Sanata Abubakar Bukola Saraki ya kai ziyara jihar Borno domin ya gani da idonsa yanayin da al'ummar jihar ke ciki sakamakon rikicin Boko Haram.

Sanata Saraki tare da wasu 'yan majalisar dattawa sun isa birnin Maiduguri inda Gwamna Kashim Shettima ya tarbe shi a filin saukar jiragen sama na birnin.

Da safiyar ranar Litinin dai, an tsaurara matakan tsaro a kewayen birnin Maiduguri domin fargabar abin da ba a so sakamakon ziyarar, ta Sanata Bukola Saraki.

A shafinsa na Twitter, Saraki ya ce manufar ziyarar ita ce su nuna wa al'ummar Borno cewar majalisar dattawa ba ta manta da su ba a cikin wannan hali da suke ciki a sakamakon rikicin Boko Haram.

Ana saran tawagar majalisar dattawan za ta ziyarci sannan 'yan gudun hijira da kuma fadar Shehun Borno.

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar dubban mutane da kuma raba miliyoyin mutane da muhallansu.