Mutane nawa ne suka je yaki a Syria ?

Hakkin mallakar hoto Reuters

Rahotanni sun nuna cewar dubban mayakan kasashen waje sun tafi gabas ta tsakiya domin su shiga kungiya mai da'awar kafa Musulunci ta IS da kuma wasu kungiyoyin na daban.

To amma kuma menene sahihancin alkaluma da ka fitar kuma a halin yanzu mutane nawa ne suke can a wadanda suka tafi?

Yanke hukuncin zuwa yaki wata kasa, wacce ta ke da nisa daga gida, ba sabon salo bane.

A shekarun 1930 kusan mutane 'yan kasashen waje 30,000 sun yi fada a yakin basasa na Spaniya kuma a farkon karni na 19, Lord Byron, Sha'iri a Biritaniya, ya yaki domin samun 'yancin kai na kasar Girka daga daular Ottoman.

A baya bayan nan da dama sun je Afghanistan da Pakistan da Iraki da Yemen da kuma Somalia.

Thomas Hegghammer, daraktan bincike a kan ta'addanci a hukumar binciken tsaron ta kasar Norway ya ce ,"Sai dai yawan masu tafiya Syria yanzu ya nuna tsananin yawan masu fada na kasashen waje wanda suka yi mubaya'a da masu da'awar jihadi a tarihi."

Yana ganin cewar, akwai dalilai da dama da su ka sa hakan.

Syria ta fi saukin zuwa a kan rikice-rikicen baya-mutane sun je kasar Turkiya da kuma gaba da iyakar ta ba tare da wata matsala ba.

Kuma da zarar an shiga Syria, wuraren da ake fuskantar hatsari basu da yawa.

Saboda kungiyar IS tana mulkin yankuna da dama, 'yan kasashen waje za su iya kaucewa mayakan sa kai wadanda suke kusa da su idan suna so.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Hegghammer ya ce "A kwanakin farko na yakin, muhimmin dalilin da aka ayyana shi ne "Ina so naje na yaki Assad na tsare 'yan Sunni da suke Syria."

Amma yanzu, muhimmin dalilin da aka fi sani shine, ina so na je daular musulinci kuma nayi rayuwa a daular."

"A Turai ma akwai mutane wadanda suke sayar da kayansu, sai su cire yaransu daga makaranta su koma Raqqa da niyar yin rayuwarsu a can".

Shirin BBC na" More or Less"

'More or Less' shiri ne da ake yada shi a gidan rediyon BBC 4 da kuma sauran tashoshin BBC.

'Yan sandan kasa da kasa na Interpol sun gano cewa mutane 4,000 wadanda suka shiga kungiyar masu tada kyar baya.

Amma kuma mutane da dama suna nuna cewar alkalumman wadanda aka sani da wadanda ba'a sani ba sun fi haka yawa.

Mayaka daga Turai da suka je Syria ko Iraki (Kiyasi)

Kasa

  • Belgium 440
  • Denmark 100-150
  • Sweden 150-180
  • Faransa 1200
  • Austria 100-150
  • Netherlands 200-250
  • Finland 50-70
  • Norway 60
  • Birtaniya 500-600
  • Jamus 500-600

Bayanai:ICSR (Jan 2015)