Kamaru ta mayar da dubban mutane Najeriya

Image caption An ce mutanen ba su da takardun shaidar zama a kamaru

Hukumomi a Kamaru sun dawo da tarin 'yan Najeriya gida wadanda aka bincika ba su da takardar shaidar zaman kasa.

Wannan dai wani mataki ne na yaki da ta'addancin da kungiyar Boko haram take haddasawa.

Mutanen wadanda yawansu ya kusa 3000, akasarinsu sun shiga Kamarun ne daga Chadi.

Yanzu haka an mika mutanen ga jami'an shige da fice.

Jamhuriyar Kamaru na daya daga cikin kasashe masu makwabtaka da Najeriya, a inda 'yan Najeriyar wadanda rikicin Boko Haram ya raba da garuruwansu, ke neman mafaka.