Boko Haram ta hallaka mutane a Kamaru

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kamaru ta tsaurara tsaro a lardin arewa mai nisa

Mutane a kalla bakwai ne suka mutu wasu kuma da dama aka yi awon gaba da su, bayan wasu hare-hare na 'yan Boko Haram a arewacin Kamaru.

An kai harin ne a kauyen Tchakarmari kusa da kan iyaka da Nigeria a cikin dare sannan kuma aka kona gidajen kauyen kurmus.

Tun bayan da harin 'yan Boko Haram ya karu a arewacin Kamaru, sai gwamnatin kasar ta sanar da tura karin dakarun 2,000 zuwa lardin arewa maso me nisa domin tabbatar da tsaro.

Gwamnan lardin kuma ya haramta saka nikabi saboda magance matsalar 'yan kunar bakin wake a yankin.

Rikicin Boko Haram ya raba mutane miliyoyi da muhallansu.