China za ta takaita sayar da makamai

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption China ta uku a jerin kasashe masu sayar da makamai a duniya

Kasar China ta sanar da cewa daga ranar 15 ga wannan wata na Agusta za ta takaita sayar da makamai ga kasashen duniya, a wani mataki na taimaka wa kanta ta bangaron tsaro.

Chinar dai ta dauki wannan mataki ne saboda fargabar da take da shi na kada makaman da za ta sayar su shiga hannun wasu kungiyoyin 'yan ta'ada na duniya.

Daga cikin kasashen da ke bukatar sayan makamai daga kasar ta China sun hada da Najeriya, Pakistan da Masar.

Wasu na ganin cewa matakin da China ta dauka ka iya shafar yunkurin da Najeriyar take yi wajen yakar 'yan Boko Haram. Sai dai kuma wasu sun musanta hakan.

China dai ita ce kasa ta uku a duniya a jerin kasashen da suke sayarwa da wasu kasashen makamai.