Obama yana fuskantar tirjiya daga 'yan majalisa

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban Amurka, Barack Obama

Shugaban Amurka Barack Obama, yana fuskantar tirjiyya da suka daga 'yan jam'iyyar Republican a majalisar kasar dangane da kaddamar da wani mataki domin yaki da sauyin yanayi.

Burin shugaban dai shi ne na rage fitar da kaso daya bisa uku na iskar gas mai guba daga cibiyar samar da wutar lantarkin kasar kafin shekarar 2030.

Sai dai kuma 'yan jam'iyyar Republican sun sha alwashin sukar shirin, suna masu bayyana firgicinsu kan cewa shirin zai dagwalgwala tattalin arzikin kasar ta Amurka ne kawai.

To amma Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar tarayyar turai sun yi maraba da wannan mataki wanda suka bayyana da wata gagarumar nasara.

Ana dai ganin cewa wannan mataki wani kalubalale ne ga sauran kasashen duniya kafin gudanar da taron kasashen kan yanayi a watan Disamba mai zuwa.