An rataye Shafqat Hussein a Pakistan

Hakkin mallakar hoto b
Image caption Shafqat Hussein

Hukumomi a Pakistan sun zartar da hukunci akan mutumin nan da aka samu da laifin kashe wani yaro dan kimanin shekaru 7 a shekarar 2004 duk da kiraye-kirayen da kungiyoyin kare hakkin dan-adam da majalisar dinkin duniya suka yi na dakatar da hukuncin.

An dai zartar wa Shafqat Hussaein hukuncin ne ta hanyar rataya inda aka rataye shi a gidan yarin dake Karachi a safiyar yau talata.

Lauyoyin sa sun hakikance cewa ya aikata laifin ne a lokacin yana da shekaru 14 da haihuwa.

Lauyoyin Shafqat din sun kuma ce an yi masa hukunci akan laifin da bai aikata ba,sai dai hukumomin sun ce ba bu wata shaida da ta nuna cewa Shafqat Hussein yana karami a lokacin da aka kama shi da laifin.

An dai bashi dama ya gana da iyalansa a ranar litinin kafin a rataye shi.