'Yan ci rani 2000 sun rasu a bahar-rum

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption 'Yan ci rani

Hukumar kula da 'yan ci rani ta duniya OIM, ta ce adadin mutanen da suka mutu a wannan shekarar a kokarinsu na tsallake tekun Bahar-rum zuwa kasashen turai, ya kai 2000.

Da yawa daga cikin mutanen sun mutu ne a tsibirin Sicily da ke tsakiyar tekun Bahar-rum, a kokarinsu na shiga kasar Italiya daga Libiya.

Hukumar kula da 'yan cirani ta duniya ta dora laifin ne a kan amfani da jiragen ruwa marasa kyau wadanda 'yan ciranin suke amfani dasu domin tsallake tekun, wanda hakan ya janyo mutuwar 'yan cirani da dama.