An kashe wani dansanda a Sokoto

Hakkin mallakar hoto Nigeria Police website
Image caption Shugaban rundunar 'yan sanda ta kasa Solomon Arase

Rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta kaddamar da bincike kan kisan wani dan sanda da aka yi a wani otal da ke babban birnin jihar.

Rahotanni sun ce dan sandan ya mutu ne sakamakon dukan da wasu ma'aikatan hotel din suka yi masa sakamakon wata hatsaniya da ta faru tsakaninsa da manajan hotel din ranar Asabar.

DSP Almustafa Sani shi ne kakakin rundunar 'yan sandan ta jihar Sokoto, ya kuma ce yanzu haka suna bincike domin gano musabbabin fadan

DSP Sani ya kara da cewa "Dole sai mun yi bincike a nutse saboda yanzu bangare daya ne kawai muka ji ta bakinsu wato ma'aikatan otal din tunda shi dan sandan ya riga ya mutu."

Tuni dai hukumar 'yan sandan jihar Sokoto ta kama mutane shida daga cikin ma'aikatan otal din da ake zargi da aikata wannan laifi na kisa.