Alkali ya kori kara kan Malema

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mr Malema ya kafa jam'iyyarsa bayan ya fice dag ANC

Alkalin wata kotu a kasar Afirka ta Kudu ya kori karar da aka dade da shigarwa a kan fitaccen dan jama'iyyar hamayyar kasar Julius Malema bisa zargin kan zargin karbar hanci.

Alkalin ya ce an jima ba a yi hukunci a kan shari'ar ba.

Wakiliyar BBC ta ce "An gaya wa masu shigar da karar su samu kwararan shaidu da za su karfafa zargin da suke yi masa idan suna so a ci gaba da gudanar da shari'ar."

A shekarar 2012 ne, aka tuhumi Mr Malema bisa zargin halasta kudaden haramun da yin cuwa-cuwa da karbar hanci a kan wata kwangila da aka bayar ta fiye da dala miliyan hudu.

Masu aiko da labarai sun ce matakin da kotun ta dauka zai yi tasiri mai kyau a kan siyarar Malema.