Ana samun rarrabuwar kawuna a Taliban

Image caption Kawunan 'yan Taliban ya rarrabu

Shugaban kungiyar Taliban reshen kasar Qatar ya yi murabus daga mukaminsa.

Hakan na zuwa ne sakamakon rashin jituwar da ake samu a baya-bayan nan bayan mutuwar shugaban kungiyar Mullah Omar.

A wata sanarwa, Syed Mohammad Tayab Agha, ya ce daga yanzu kungiyar ta Taliban ta dinga aiwatar da duk wasu al'amuranta daga kasar Afghanistan kawai, ciki kuwa har da nadin sabon shugaban da ta yi.

Amma a sanarwar Syed Mohammad bai ambaci sunan sabon shugaban Taliban da aka nada a makon da ya gabata ba, bayan taron kwamitin zartarwa da kungiyar ta yi a Pakistan.

Wasu manyan jagororin kungiyar sun ce ba a shawarce su ba kafin a nada sabon shugaban.