Amurka za ta sayar wa Nigeria makamai

Hakkin mallakar hoto Nigeria government
Image caption Shugaba Buhari yayin da ya kai wa shugaba Obama ziyara

Amurka ta ce za ta sassauta dokar Leahy da ta kakaba wa Najeriya na kin sayar mata da makamai.

Dokar Leahy dai wata dokar 'yancin dan adam ce ta Amurka wadda ta hana kwamitin harkokin wajen kasar taimaka wa sojojin duk wata kasa da aka kama da laifin cin zarafin bil'adama.

Dan majalisar dokokin Amurka Darrel Issah, shi ne ya bayyana hakan bayan ya gana da manyan hafsoshin sojin Najeriya da jami'an ma'aikatar tsaro a Abuja.

Mista Issah -- wanda shi ne ya jagoranci tawagar 'yan majalisun dokokin Amurka da suka kawo ziyara Najeriya, ya ce an tattauna a kan al'amura da dama musamman a bangaren hada karfi domin yakar kungiyar Boko Haram.

Makonni biyu da suka gabata ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya kai ziyara Amurka inda ya bukaci gwamnatin kasar da ta dage wannan doka a kan Najeriya domin kasar ta samu damar sayan makamai.