An gano motar sata bayan shekaru 22

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan sandan Afrika ta kudu.

Wani dan Afrika ta kudu ya samu motarsa bayan an sace ta shekaru ashirin da biyu da suka wuce.

An samo motar kirar Toyota ta Derrick Goosen a garin Pretoria, kuma lafiyar ta kalau.

'Yan sandan yankin Limpopo sun tsare motar a wurin wasu shingayen bincike kuma aka kwashe watanni da dama ana cigiyar mai motar saboda an goge lambar inji da kuma na motar.

Mr Goosen ya yi wa 'yan sandan godiya saboda kwazonsu.

An saba satar motoci a Afrika ta kudu, inda motoci da dama aka sa masu na'urar da za ta nuno duk inda suke.