Facebook ya yi karya

Image caption Green Hank kenan

Wani mai yada labarai ta kafar intanet wato blogger, Hank Green, wanda kuma daya ne daga cikin taurarin da suka fi shahara ne a kafar You Tube, ya soki lamirin kamfanin sada zumunta na Facebook da cewa ya yi zulaken yawan mutanen da suka kalli hotuna masu motsi a kafar.

Ya kuma kara da zargin Facebook din da gaza magance satar fasaha ta hotuna masu motsi.

A wani rubutu da ya yi ta kafar yada labaran nasa, Mista Green ya ce duk da cewa Facebook dandalin hotuna masu motsi ne da ke kayatarwa, kamfanin bai girmama ingancin hotuna masu motsi saboda zulaken yawan mutanen da ya ce sun kalli hotuna a watan Aprilu akan Facebook.

A watan Aprilu ne dai kamfanin na Facebook ya fadi cewa mutane biliyan hudu ne suke kallon hotuna masu motsi a shafin a kowace rana.

Sai dai Mista Green ya ce wannan batu karya ne domin kallon hoto na tsawon dakika uku ba kallo ba ne.

Ya kuma kara da sukan kamfanin bisa zargin satar hotuna daga wasu shafukan da ba nasu ba.

A watan June, wani bincike da wani kamfanin tallace-tallace na Ogilvy ya yi ya nuna cewa kaso 73 na hotunan da Facebook ya ke amfani da su ana dauko su ne daga wasu shafukan ne.

Sai dai kuma kamafanin na Facebook ya mayar wa da mista Green martani ta kafar yada labaran nasa.

Image caption Green Hank ya ce mutanen da Facebook ya ce sun kalli hounansa masu motsi karya ce

Kmafanin ya ce yana matukar girmama irin wahalar da muane suke sha wajen kirkirar abubuwa saboda haka ba zai yi satar fasaha ba.