Da wuya a samu mai rai a tekun Bahar Rum.

Hakkin mallakar hoto msf
Image caption 'Yanci ranin da aka ceto

Masu aikin ceto a tekun Bahar Rum sun ce sun fitar da rai daga samun wani da rai a cikin mutanen da wani jirgin ruwa ya nutse da su a kusa da kasar Libiya.

Jirgin da ya nutse ya na dauke da 'yanci rani 600 ne a cikin sa.

Masu tsaron tekun Italiya da kuma hukumar dake kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya sun ce ya zuwa yanzu an ceto mutane 400, yayin da aka gano gawawwaki 25.

Jiragen ruwa bakwai da kuma jirage masu saukar ungulu ne suka isa wurin domin aikin ceton.

Jami'ar yada labaran hukumar dake kula da 'yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya Melissa Fleming, ta ce mutane ne suka yi yawa a jirgin da ya nutse din.

'Yan ci-rani sama da 2,000 ne ake zaton sun nutse a tekun a wannan shekarar, a yunkurin su na tsallaka tekun zuwa Turai.