Ana kokarin sasanta rikicin PDP

Image caption Jam'iyyar PDP ta sha kaye a zaben 2015 bayan shafe shekaru 16 tana mulki

Shugabannin jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya sun ce suna kokari sasanta rashin jituwar da ta kunno kai a jam'iyyar.

Rikicin ya samo asali ne tsakanin tsakanin ma'aikatan sakatariyar jam'iyyar da shugabanin zartarwarta, inda har ta kai ma'aikatan yunkurin hana duk wani dan kwamitin zartarwarta shiga harabar sakatariyar jam'iyyar.

Wannan dai ya biyo bayan wani shiri da shugabanin suka fito da shi na rage ma'aikatan da kashi 50 da kuma zaftare albashinsu.

Sai dai daga bisani duka bangarorin sun ce sun cimma 'yar kwarya-kwaryar jittuwa bayan sa-bakin da kwamitin amintattu na jam'iyyar yayi.

Kungiyar kula da jin dadin ma'aikatan sakatariyar jam'iyyar dai ta ce 'yan kwamitin gudanarwar jam'iyyar ne ya kamata su bar aiki saboda a cewarta basu da aiki sai facaka da kudin jam'iyya.

Rahotanni dai sun nuna cewa kwamitin amintattu da kwamitin koli na jam'iyyar sun wato BoT da NEC sun marawa ma'aikatan baya wajen kira ga 'yan kwamitin gudanarwa NWC da su ajiye mukamansu, suna zarginsu da cewar sun jagoranci shan kayen da jam'iyyar ta yi a zaben 2015.