Cin yaji da yawa yana iya sa tsawon rai

Image caption Cin abinci mai yaji na iya sa tsawon rai

Wani bincike da aka gudanar a kasar China ya nuna cewa cin abinci mai yaji, musamman danyen borkono, zai iya taimakawa mutane su yi tsawon rai.

Masu bicike a Bejin babban birnin China sun yi nazari kan dabi'ar cin abinci ta mutane rabin miliyan a kasar cikin shekaru bakwai.

Binciken ya nuna cewa wadanda suke cin abinci mai yaji sau daya a mako sun fi fuskantar hadarin mutuwa fiye da wadanda suke ci kullum.

Masu binciken sun ce sakamakon da aka gano din ya ta'allaka ne da zallar sanya ido da lura da aka yi sun kuma yi kira da a zurfafa binciken a wasu wuraren.

Amma sun lura cewar ainihin 'ya'yan barkono a can baya an taba samun su da sinadaran kare garkuwar jiki.