Kamfanin EE ya ce a dawo da na'urar cajin waya

Image caption Chajar Power Bar ta Kamfanin EE

Kamfanin wayoyin salula na EE, ya bukaci da a dawo masa da 'yar karamar na'urar caja wayar da ya bayar kyauta bayan wani dalibi dake karatun aikin likitanci ya kone a lokacin da yake amfani da daya daga cikin cajojin.

Kamfanin ya ce ya gano irin wadannan matsaloli na konewar mutane sakamakon amfani da cajar guda biyar.

EE ya ce wannan matsala na faruwa ne saboda zafin da cajar wayar ke yi, kuma ya ce ya bayar da irin wadannan cajoji guda kusan dubu 500.

Domin sakawa wadanda wannan tsautsayi ya rutsa da su, kamfanin ya ce zai basu kyautar fam 20 domin su sayi kayan amfanin wayoyi.

A cikin wata sanarwa, Kamfanin ya ce sun gano wasu 'yan hadurra da suka faru da cajarsu samfurin E1-06.

Dalibar Katy Emslie daga Aberdeen ta kone ne bayan da cajar wayar ta tayi bindiga lamarin da ya haifar da tashin gobara a dakinta.

EE ya fara raba kyautar cajar ta sa ne ga abokan huldarsa tun a watan Aprilu.

Ya kuma bai wa masu sayan kayansa damar kawo wayoyinsu marasa caji a basu mai caji cikakkiya.

An kirkiro da wannan na'urar cajin ne da akafi sani da power bank, bayan da bincike ya gano cewa kusan kaso 60 cikin 100 na na'urorin tafi da gidanka batiransu basa yin cikakken yini guda da caji.