Birtaniya za ta taya Najeriya yakar Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AFP

Biritaniya ta sake tabbatar da anniyar ta na taimakawa Najeriya wajen yakar 'yan ta'adda.

Lieutenant General Gordon Messenger, mataimakin babban hafsan sojoji a kan dabaru da ayyuka na Biritaniya, ne ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da shi da wasu manyan jami'an soji na Biritaniya su ka kai ziyara offishin Manjor janar Gabriel Olonisaki, babban hafsan hafsoshin soji na Najeriya.

Laftanan janar Messenger ya ce manufar ziyarar manyan jami'an sojin na Biritaniya zuwa Najeriya ita ce ta fadada da kuma sake karfafa dangantaka tsakanin jami'an tsaron kasashen biyu.