Akwai yiwuwar ambaliya a Nigeria

Hakkin mallakar hoto wiki
Image caption Shugaban hukumar NEMA, Sani Sidi

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya wato NEMA, ta gargadi al'ummomin da ke zaune a kusa da kogin Benue da su tashi domin akwai yiwuwar samun ambaliyar ruwa daga nan zuwa watan Nuwamba.

A wata sanarwa da kakakin hukumar Sani Datti ya fitar, hukumar ta ce sun samu bayanai daga hukumomin jamhuriyar Kamaru cewa daga yanzu zuwa watan Nuwamban za a rinka sakin ruwa daga dam din Lagdo na kasar ta Kamaru saboda timbatsar da ya yi.

A saboda haka ne hukumar ta yi kira ga mazauna yankunan da su kula.

Ta kuma kara da kira ga hukumomi da su kwashe mutanen yankunan domin gudun asarar rayuka da dukiyoyi.

Kazalika, wasu masana kan ayyukan kai daukin gaggawa da kiyaye annoba na nuni da zubar da shara a ko ina musamman a cikin Magudanan Ruwa a matsayin wata babbar dabi'a da ke haifar da ambaliyar ruwa a garuruwa da Birane.

Masana dai na ganin karfafa dokokin zubar da shara ko Bola barkatai na cikin hanyoyin da za a magance wannan matsala wacce ke ci gaba da afkuwa kowacce shekara.