Maza za su fara hutun haihuwa a Najeriya

Hakkin mallakar hoto wiki
Image caption Gwamnan jihar Enugu, Lawrence Ifeanyi Igwuanyi

Gwamnatin jihar Enugu da ke kudu maso gabashin Najeriya, ta bullo da wani sabon tsari na bayar da hutun makwanni uku ga maza ma'aikata idan matansu sun haihu.

Gwamnatin dai ta ce hakan wani mataki ne da jihar ta dauka na bai wa mazajen dama domin su taimaka wa matan nasu yadda ya kamata.

Su ma mata ma'aikatan jihar an ware musu hutun watanni shida idan sun haihu, sabanin watanni uku da gwamnatin tarayya da wasu jihohi suke bayarwa.

Ba kasafai dai ake bayar da irin wannan hutu na haihuwa ga maza ma'aikata a Najeriya ba.