Me ake ciki game da zaben shugaban PDP?

Image caption Jam'iyyar PDP ta zamo babbar jam'iyyar adawa a Najeriya

A Najeriya, tun bayan mummunan kayen da jam'iyyar adawa ta PDP ta sha a zabukan da aka yi a watannin Maris da Aprilu inda mulkinta na shekaru 16 a jere ya kawo karshe, jam'iyyar take cikin rudani.

A watan Mayu ne, shugaban jam'iyyar, Alhaji Ahmadu Adamu Mu'azu ya yi murabus, al'amarin da yasa aka kafa shugabancin rikon kwarya na watanni uku karkashin jagorancin Alhaji Halliru Muhammad.

To yanzu watanni uku na sharadin rikon kwaryar na gab da cika, kuma batun maye gurbin shugaban jam'iyyar ne ya sake tasowa.

Sai dai wasu na ganin cewa dole ne kujerar shugaban jam'iyyar ta fito daga arewa maso gabashin kasar tunda tsohon shugaban, Ahmad Mu'azu murabus ya yi kafin wa'adinsa ya cika.

Kimanin mutane 20 ne dai suke takarar neman shugabancin jam'iyyar a halin yanzu.

Yanzu dai PDP ita ce babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, bayan da jam'iyyar APC ta karbi mulki daga hannunta a zabukan da aka yi a watannin baya.