An hana mayar da sadaki a Uganda

Kotun koli ta Uganda ta hana mayar da sadaki, inda ta ce yin hakan ya sabawa tsarin dokokin da a ke bi na aure a kasar saboda haka ya kamata a dakatar.

Alkalin ya ce hakan na nuna tamkar an mayar da mata wata haja ce a kasuwa kuma hakan yana shafar 'yancin mata wajen saki.

Amma kuma sun yi watsi da bukatar cewa kudin sadaki ya sabawa doka.

Masu fafutika sun ce sadaki yana mayar da mace mallakin mijinta.

Idan har aure ya mutu a Uganda, a da ana sa ran matar ta mayar da sadaki -- wanda sau dayawa ake biya da dabbobi.

Amma kuma anyi jayayyar cewar, kamar yadda mata basu kai mazajensu arziki ba, da dama sun samu kansu a zamantakewar aure mara dadi.

Kungiyar da ke kula da 'yancin mata ta Mifumi ce ta kai karar, wacce ta ce sadaki yana karfafa zalunci a gidaje.