Wanne kulob ne ya fi farin jini a gasar premier Ingila a Afrika?

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Gasar da Afrika ta fi so

Ga masoya kwallon kafa a Afrika, gasar premier ta Ingla ita ce kan gaba, kuma kofin gasar suka fi bai wa fifiko.

Biliyoyin mutane ne a duniya suke bibiyar gasar premiyar ta Ingla, kuma miliyan 260 daga cikin wadannan mutane suna Afrika.

A yayinda ake fara gasar ta shekarar 2015-16, gidajen kwallo kama daga birnin Cape Town zuwa Alkahira zasu shirya tarbar masoya wasan da dama, wadanda suke shirin kallon wasan a manyan allunan talabijin.

Amma kuma wanne klub ne ya fi fice a nahiyar?

Ba lallai ba ne mu iya bayar da cikakkiyar amsa ba, duk da cewa binciken da shafin sada zumunta na twitter ta yi, ya sa an dan fahimci inda ra'ayoyin mutane suka karkata. Shafin ya duba yawan mutane da ke bibiyar shafukan kulob-kulob din da ke twitter, daga nan ya kakkasa su don ganin waye ya fi magoya baya.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Bisa wannan tsari, babu shakka kulob din Chelsea aka fi so a nahiyar Afrika.

Ba za a iya maganar gasar premier a Afrika ta yamma ba tare da an ambato Didier Drogba da Solomon Kalou da Samuel Eto'o da Victor Moses da Micheal Essien da kuma John Mikel Obi ba, duk 'yan yankin Afrika ta yamma ne, wadanda suka bugawa kungiyar Chelsea.

Duk da haka, Drogba ya fi yin fice saboda nasarorin da ya samu a wasan kwallon kafa.

Tabbas, fitaccen dan wasan kulob din ne, wanda shi ne ya ci bugun fenareti a gasar zakarun turai da Chelsea ta lashe a shekarar 2012 kuma shi ne dan wasan Afrika na farko da ya cimma nasarar cin kwallaye 100 a gasar premier Ingila.

Amma kuma an fi martaba shi a kasar sa ta haihuwa Ivory Coast, saboda kokarinsa na samar da zaman lafiya a kasar bayanda rikici ya barke a kasar a shekarun 2010-2011, kuma ya kafa wata gidauniya ta ingnta lafiya da kuma ilimi a kasar.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

A yankin gabashin Afrika, Arsenal ce ta yi fice. Za a iya dangata shaharar Arsenal da 'yan wasan nan da ake kira da 'invincibles', wadanda suka taka leda a kakar 2003-04, kuma suka lashe gasar ba tare da an ci su wasa ko daya ba a wassanin 49 da ba a doke su ba.

Irin rawar da 'yan wasan kwallon kafa na Africa kamar Nwanko Kanu da Emmanuel Adebayor da Kolo Toure sun sa kulob din ya kara farin jini. Tabbas Kanu shine silar ficen da Arsenal ya yi a Najeriya.

Amma kuma abin mamaki shi ne, dan kasar Kenya daya ne kacal daga yankin Gabashin Afrika ya taba buga wasa a gasar premier. Dan wasan ko shi ne Victor Wanyama wanda ya yi wasa a Southampton.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Ba abin mamaki bane da klub din Manchester United ya fi yin fice a Kudancin Africa.

Su ne kulb din da suke fi kowacce nasara a tarihin gasar premier ta Ingila, inda suka ci nasarar lashe kambun sau13 tun da aka fara gasar a shekarar 1992.

Sun kuma dauki Quinton Fortune, daya daga cikin manyan 'yan kwallon kafa na Africa ta Kudu, ya kuma bugawa klub din Manchester United kwallo har tsawon shekaru bakwai.

Kuma yana cikin tsofofin 'yan wasa wadanda sukn ziyarci nahiyar a matsayin jakadun kulob din a kowacce shekara.

Afrika ta kudu ita ce kasa ta farko a Afrika da ta ke da kungiyar magoya bayan klub din Manchester United wanda kungiyar ta Ingila ta san da su.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Ga 'yan Arewacin Afrika kuma, un fi son klub din Arsenal. 'Yan klub din Arsenal wanda ake yiwa lakabi da "gunners" suna da magoya baya dayawa a Morocco da Algeria da kuma Tunisia.

Kungiyoyin magoya bayan Arsenal din sun taimaka wajen kara farin jinin Arsenal din ta hanyar shirya gasannin da za su kara farin jinin kulob din a kowacce shekara.

Amma a Masar, klub din Chelsea ne ya fi yin fice sakamakon dan wasan kasar Mohamed Salah da ya koma kungiyar a shekarar 2014 a kan kudi dala miliyan 17.