Mutanen da suka tsira a teku sun isa Italiya

Hakkin mallakar hoto msf
Image caption 'Yanci ranin da aka ceto a baharrum

Fiye da mutane 300 wadanda suka samu tsira daga hadarin kwale-kwalen da ya tuntsire a kogin bahar Rum kusa da kasar Libiya a ranar Laraba sun isa Italiya.

Jirgin sojin ruwan kasar Ireland ne ya dauke su zuwa birnin Parlemo.

Jirgin sojin ruwan kasar Ireland ya isa birnin na Perlemo da yammacin ranar Alhamis dauke da wadanda aka ceta daga kogin Libiya su 367.

A cikinsu kuma akwai mata 13 da kananan yara 12.

Kungiyar likitoci ta Médecins Sans Frontières ta shaida wa BBC cewa ta samu a kalla gawawwaki 25.

A ta bakin mai magana da yawun hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Barbara Molinario, ta ce wadanda suka tsiran sun fito daga kasashen Syria da Bangladash da Eritrea sannan akwai wasu da dama daga kasashen da ke kudu da hamadar sahara ta Afirka .

An kuma tallafa musu da abubuwa kamar abinci da ruwan sha da tufafi da kuma magunguna.