An sassara mai rubutu a intanet Niloy Neel

Hakkin mallakar hoto Facebook
Image caption Niloy Neel mai rubutu a intanet

'Yan sanda a Dhaka babban birnin kasar Bangladesh sun ce an sassara mutumin nan da ya shahara wajen yin rubutu a intanet wanda kuma bai yarda da wanzuwar Ubangiji ba har lahira.

Wasu 'yan bindiga ne dai suka kai hari a gidan Niloy Neel da ke birnin Goran inda suka sassara shi da adda.

Shi ne dai mutum na hudu da ke rubutu a intanet wanda ba ruwansu da addini da aka kashe a cikin shekarar nan inda ake zargin masu da'awar musulunci dauke da makamai a Bangladesh da aikatawa.

Editan BBC a kudancin Asiya Charles Haviland ya ce kamar sauran wadanda aka kashe da suka yi suna wajen rubutu a intanet, Mr Neel ba wai bai yarda da addini ba ne kawai, bai yarda da wanzuwar Ubangiji ba ma.

Niloy Neel dan asalin addinin Hindu ne ba musulmi ba ne shi.

Dukkan mutane hudun da aka kashe suna cikin jerin sunayen mutane 84 da ke rubutu a intanet wadanda ba su yarda da wanzuwar Ubangiji ba wanda kungiyoyi masu da'awar musulunci suka rubuta su a shekarar 2013 tare da rarrabawa.

An dai mikawa gwamnati takardar jerin sunayen da nufin a kama tare da tsare irin wadannan mutanen dake rubutu a intanet inda suke kokarin yin sabo.

Sai dai kungiyoyin da suke bukatar a kama irin wadannan mutane masu rubutu a intanet din sun ce ba su da masaniya akan wadanda ke da hannu akan kashe-kashen da ake yi wa irin wadannan mutane.