Malaman jami'a sun fara yajin aiki a Ghana

Image caption Marasa lafiya suna cikin tsaka mai wuya

Malaman jami'oi a kasar Ghana sun shiga yajin aikin sai baba-ta-gani, domin neman a biya musu wasu kudaden ariya na alawus-alawus din gudanar da bincike.

Gwamnatin shugaban Ghanan Draamani Mahama na fama da yaje-yajen aikin ma'aikata da suka hada da likitoci a fadin kasar da suma ke neman a biya musu wasu bukatu.

kazalika, a ranar Juma'a ne likitoci a kasar Ghanan suka dakatar da bayar da taimakon gaggawa ga marasa lafiya a ci gaba da yajin aiki da suke yi.

Amma gwamnatin kasar ta ce ta dauki matakai domin shawo kan wannan matsala.

Ta ce ta bai wa shugabannin asibitoci -- wadanda suma likitoci ne, umarnin kula da marasa lafiya masu bukatar taimakon gaggawa sannan kuma ta ce tana tuntubar likitoci masu asibitocin kansu.

Tun a makon da ya gabata ne dai likitocin suka fara yajin aiki bayan rashin daidaituwa da suka samu da gwamnatin kasar a kan inganta yanayin aikinsu.