'Yan bindiga sun kashe sojoji a Bayelsa

An kashe soji a kai harin Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rahotanni na cewa bayan kai harin 'yan bindigar sun kwashe makaman jami'an tsaron

Rahotanni na cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari a wajen binciken abababen hawa a Nembe a jihar Bayelsa sun kuma hallaka sojoji hudu.

'Yan bindigar sun kuma dauke makaman su, wadanda suka hada da kananan bindigoi da kuma wata bindiga mai sarrafa kanta wacce aka girke a wurin.

Laftanar Kanar Ado kakakin rundunar tsaro ta JTF a yankin Naija Delta ya tabbatar da labarin kai harin ga wakilin BBC amma bai ce komai ba game da kashe sojojin.

Babu kungiyar da ta dauki alhakkin kai harin.

A baya dai yankin na Niger Delta mai arzikin mai ya sha fama da hare-hare daga 'yan kungiyar fafutuka ta yankin masu gwagwarmaya da makamai